Tinubu ya nemi goyon bayan kafafen yada labarai kan kudirin dokar haraji
Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya bukaci goyon bayan kafafen yada labarai kan kudirin sake fasalin harajin kasar, yana mai bayyana hakan a matsayin wani muhimmin mataki na gina kasa da kuma wadata ga yan Najeriya.
Shugaban wanda ya samu wakilcin Ministan Yada labarai na kasa, Mohammed Idris, ya yi wannan bayani ne a Lagos
Ya kara da cewa duk da banbancin ra'ayi a tsakanin al'umma game da dokar haraji, amma akwai bukatar yin garambawul ga tsarin tafiyar da haraji a halin yanzu.
Ya jaddada kwarin gwiwar cewa, tattaunawar da ake yi kan sauye-sauyen haraji, za a samu mafita.