Tinubu ya kaddamar da aikin ziyarar mabiya addinin kirista zuwa Isra'ila, Jordan na 2024


 Tinubu ya kaddamar da aikin zyarar mabiya addinin kirista zuwa Isra'ila, Jordan na 2024

Shugaban Nijeriya Bola Ahmad Tinubu ya kaddamar da ziyarar ibadar mabiya addinin kirista zuwa kasashen Isra'ila da Jordan na 2024

Bola Ahmad Tinubu wanda Sakataren gwamnatin tarayya, Sanata George Akume ya wakilta, ya bukaci mabiya addinin na kiristanci  da su dauki tafiyar a matsayin wata dama ta karfafa imaninsu.

Hakan na kunshe  ne a cikin wata sanarwa da shugaban yada labarai da hulda da jama'a, Celestine Toruka, ya fitar a shafin Hukumar NGChrisPilgComm, na  X, a ranar Litinin.

An kaddamar da jigilar ne a ranar Lahadi a Alausa, Ikeja, jihar Legas.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp