A karshen watan Satumba ne shugaban na Nijeriya ya aike da sunan Ambassador Haruna Ginsu a matsayin shugaban hukumar gudanarwa ta sabuwar hukumar ta Northwest Development Commission tare da nada Senata Tijani Yahaya Kaura da Hon. Abdulkadir S. Usman a matsayin mambobi. Sai dai sanarwar da fadar shugaban kasa ta fitar ta baya-bayan nan ta ce Shugaba Tinubu ya musanya sunayensu da Ja'afar Abubakar Sadeeq da Yahaya Aminu Abdulhadi, yayin da ya ayyana Lawal Samaila Yakawada a matsayin shugaba. Sai dai sanarwar ta ce har yanzu Farfesa Abdullahi Shehu Ma'aji shi ne manajan daraktan hukumar
Tinubu ya janye nadin da ya yi wa Ambassador Haruna Ginsu da sauran wasu mukamai
DagaAhmadu
-
0