Tayoyin motocin fadar shugaban kasa da gina ofisoshi za su lakume naira biliyan 15 kasafin kudin 2025 - Jaridar Punch


An ware naira biliyan 15.09 domain sayen tayoyin motocin fadar shugaban kasa da kuma gina ofisoshi na mataimaka da masu baiwa shugaban kasa shawara.

Hakama an ware naira biliyan 5.49 domin gyare-gyare a fadar ta shugaban kasa cikin shekara daya.

Wadannan bayanan dai na kunshe a cikin kasafin kudin shekara ta 2025 da shugaban kasa Bola Tinubu ya gabatar, wanda aka fitar da bayanan ga al'umma a yau Alhamis, inji jaridar Punch.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp