Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu da mataimakinsa Kashin Shettima za su kashe naira biliyan N9.36 domin yin tafiye-tafiye na cikin gida da waje da kuma ciye-ciye da tande-tande a shekara ta 2025.
Wannan na kunshe ne a cikin bayanin kasafin kudin bana da ofishin ministan kasafin kudi da tsare-tsaren tattalin arziki ya fitar.
A cewar jaridar Dailytrust shugaban kasa Bola Tinubu zai kashe naira biliyan N7.44 yayinda mataimakinsa Kashim Shettima zai kashe naira biliyan N1.9.
Category
Labarai