Mai horar da tawagar Super Eagles B Augustine Eguavoen, ya gayyaci yan wasa 30, don bugawa Nijeriya wasa da kasar Ghana a wasan share fagen shiga gasar cin kofin Nahiyar Afrika ta yan wasan cikin gida.
Gasar wadda ita ce karo na 8 za ta gudana daga farkon watan Fabrairun 2025 a kasashen Kenya da Uganda da kuma Tanzania.
Tuni yan wasa 30 irinsu Rabiu Ali, na Kano Pillars da ya ci kwallo 8 a kakar bana, da yan wasa irinsu Musa Zayyad na Elkanemi da kuma dan wasan Rivers United Steven Mayo suka samu goron gayyata don buga wasan.