Sufeta Janar na 'yan sandan Nijeriya Kayode Egbetokun, ya bayarda umurnin yin bincike kan zarge-zargen cin zarafi da kisa da kuma kama masu zanga-zangar matsin rayuwa da ta faru a fadin kasar.
Kungiyar kare hakkin bil adama ta Amnesty International a cikin wani rahoto da ta fitar a kwanannan, ta zargi rundunar 'yan sanda da amfani da karfin da ya wuce iyaka a yayin zanga-zangar matsin rayuwa da ta faru daga 1 zuwa 10 ga watan Augustan 2024, da yayi sanadiyar mutuwar mutum 24 a jihohin Borno, Kaduna, Kano, Katsina, Jigawa da kuma Niger.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun rundunar ACP Olumiyiwa Adejobi ya fitar a Abuja, ya ce akwai alamun shakku da kuma karya a zargin da Amnesty International ta yi, inda ya ce Kayode Egbetokun ya bada umurnin yin bincike domin gano gaskiyar lamari.
Category
Labarai