Dakarun sojin Nijeriya da ke yankunan arewa maso yamma da arewa ta tsakiyar Nijeriya sun kama wasu shugabannin 'yan ta'adda, da suka hada da Hamisu Sale wanda aka fi sani da Master da Abubakar Muhammad, sai Bako Wurgi, wani makusancin Bello Turji.
Daraktan yada labarai na hedikwatar tsaron Njieriya Manjo Janar Edward Buba, ne ya tabbatar da hakan a wata sanarwa da ya fitar yau Jumu'a kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito
A cewar sanarwar, Wurgi, wanda ake zargi da kisan Sarkin Gobir a Sokoto ya samu raunin harbi da dama lokacin wata arangama da jami'an tsaro, kafin daga bisani su kama shi.
Category
Labarai