Runduna ta 1 ta dakarun rundunar haɗin gwiwa ta Operation Fansan Yamma, ta hallaka 'yan bindiga da dama a jihar Zamfara, ciki har da wani kasurgumin dan bindiga Alhaji Ma’oli.
A yayin wani farmaki da ta kai ne a kauyen Mai Sheka kusa ga kauyen Kunchin Kalgo, rundunar ta gama da ɗan ta'adda Ma’oli, wanda ya yi suna wajen kakabawa al'ummomi haraji da suka hada da Unguwan Rogo, Mai Sheka, Magazawa, da yankunan Bilbis cikin karamar hukumar Tsafe.
Wani bayani da Kodinetan yada labarai na
Rundunar Operation Fansan Yamma, Kanal Abubakar Abdullahi ya fitar, ya ce an kai harin ne bayan samun bayanan da suka nuna cewa an ga 'yan bindigar saman babura a yankin karamar hukumar Tsafe.