Majalisar zartarwa ta Nijeriya ta amince da sauya sunan jami'ar Abuja zuwa jami'ar Yakubu Gawon.
Ministan yada labarai Muhammed Idris ne ya bayyana hakan bayan zaman majalisar da Shugaba Tinubu ya jagoranta.
Ministan ya ce wannan wani mataki ne na girmama tsohon shugaban kasar Yakubu Gowon, kuma za a tura zuwa majalisar dokoki domin tabbatarwa.
Category
Labarai