Shugaban mulkin soja na Burkina Faso ya yi wa fursunoni sama da 1000 afuwa


Shugaban kasar Burkina Faso Kyaftin Ibrahim Traore ya yi wa fursunoni sama da dubu daya afuwa a ƙasar.

Kusan fursunoni 400 an yafe musu laifuffukansu tare da sakin su, wasu 750 aka rage musu yawan lokacin da za su shafe a gidan kaso, yayin da wasu fursunoni uku aka rage musu hukunci daga kisa zuwa hukuncin rai da rai.

Wannan afuwa dai, kamar yadda kafar yada labarai ta TRT ta ruwaito, shugaban ya yi ta ne albarkacin sabuwar shekarar 2025.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp