Luiz Inacio Lula De Silva |
An yi wa shugaban kasar Brazil Luiz Inacio Lula De Silva tiyata sakamakon taruwar jini a kwakwalwarsa sanadiyar faduwar da ya yi a baya-bayan nan.
A wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na Instagram a ranar Talata, wani asibiti mai suna Syrian-Lebanese da ke Sao Paulo na Brazil ya tabbatar da hakan.
A cikin sanarwar asibitin ya ce tun a daren ranar Litinin ne aka kammala aikin ba tare da wata matsala ba, kuma yanzu haka shugaban kasar ta Brazil yana cikin yanayi mai kyau inda yake ci gaba da samun sauki.
Category
Ketare