Sanarwar fadar shugaban kasa ta wannan Asabar ta ce, shugaban na Nijeriya, ya soke nadin da ya yi wa daraktoci uku a sabuwar hukumar ta Southeast Development Commission tare da janye nadin Donatus Eyinnah Nwankpa daga cikin mambobin da za su rika kula da hukumar.
Sai dai shugaban ya ce kamar yadda ya sanar tun da farko Hon. Mark C. Okoye shi ne zai jagoranci hukumar a matsayin manajan darakta idan har Majalisar Dattawa ta tabbatar da nadin da aka yi musu.
Shugaban tuni ya sanar da sabbin sunayen jami’an da za su maye gurbin wadanda ya warware nadinsu