Shugaban Nijeriya Bola Ahmad Tinubu ya nuna jin dadinsa da sake bude matatar mai ta Warri da aka gyara da kamfanin na kasa NNPCL ya yi.
Wani bayani da mai magana da yawun shugaban Bayo Onanuga ya fitar a wannan Litinin, Shugaba Tinubu ya bayyana wannan a matsayin babbar nasara ce da za ta kara karfafa gwuiwar 'yan Nijeriya.
Gyara matatar mai ta Warri na zuwa ne, yan kwanaki bayan da matatar mai ta Fatakwal ta fara aiki.