Shugaba Bola Tinubu na Nijeriya ya umurci ma'aikatar shari'a da majalisar dokokin kasar su magance korafe-korafen da suka taso dangane da kudirin dokar haraji.
Tun bayan gabatar da wannan kudurin na garambawul ga dokar haraji gwamnatin Tinubu ke shan suka, lamarin da ya sa gwamnonin arewa su ka juyawa Tinubu baya tare da yin watsi da wannan dokar.
Gwamnonin sun yi zargin cewa dokar za ta baiwa wasu jihohin fifiko tare da mayar da yankin arewa baya.
Sai dai ministan yada labarai Mohammed Idris ya ce shugaban kasa ya ji korafe-korafen da 'yan ƙasar ke yi kuma ya umurci majalisa da ma'aikatar shari'a da sauran masu ruwa da tsaki su yi aiki tare don gyara dokar.