Shugaba Tinubu ya amince da sufuri a jiragen kasa kyauta ga 'yan Nijeriya


A kokarin saukaka zirga-zirga a lokacin bukukuwan Kirsimeti, Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya amince da sufurin jiragen kasa kyauta ga 'yan kasar daga ranar 20 ga watan Disamban 2024 zuwa 5 ga watan Janairu 2025.

Ministan yada labarai na tarayya Mohammed Idris, shi ne ya bayyana hakan a Abuja, bayan taron majalisar zartarwa na ƙasar.

Muhammad Idris ya ce wannan zai saukaka wa 'yan Nijeriya musamman marasa karfi a bangaren kashe kudaden sufuri.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp