Gwamnan jihar Bauchi Bala Muhammad Kaura ya bukaci Shugaba Tinubu da ya dakatar da dokar garambawul ga haraji saboda za ta iya kawo hargitsi.
Gwamnan ya yi wannan kiran ne a yayin bukin Kirsimeti da aka shirya a Bauchi.
A cewar Gwamna Bala, babu ta inda dokar za ta amfani mutanen arewa, inda ya kara da cewa gwamnoni ba za su iya biyan albashi ba.
Category
Labarai