Shugaban Nijeriya Bola Ahmad Tinubu da gwamnonin kasar da shugabannin majalisa da wasu jagorori sun yi kira da a rungumi son juna, zaman lafiya da kuma hadin kai, a daidai lokacin da mabiya addinin kirista ke bukukuwan Kirsimeti a fadin duniya.
Shugabannin sun kuma bukaci 'yan Nijeriya da su yi addu'a ga masu mulkin kasar domin dorewar ci gaban kasar.
Daga cikin wadanda su ka yi wadannan kiraye-kirayen har da kakakin majalisar wakilai Abbas Tajuddeen, mataimakin shugaban majalisar dattawa Sanata Barau Jibril, tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, da kuma gwamnonin Kwara, Gombe, Bauchi da Nasarawa da dai sauransu.
Category
Labarai