Sau 190 aka soke tashin jiragen sama na cikin gida a Nijeriya cikin watanni biyu - Hukumar kula da sufurin sama ta NCAA


Hukumar kula da sufurin jiragen sama ta Nijeriya ta nuna damuwa akan yadda ake samun karuwar dakatarwa ko dage tashin jiragen sama na cikin gida a yan kwanakinnan.

Mukaddashin darakta janar na hukumar Kyaftin Chris Najomo, ya bayyana cewa daga cikin jirage 5,291 da suka tashi a watan Satumban 2024, an dage tashin jirage 2,434 yayinda aka dakatar da 79.

A yayin wani taron masu ruwa da tsaki a Abuja, Kyaftin Chris ya ce a cikin watan Oktoba jirage 2791 aka dage tashinsu, yayinda aka dakatar da jirage 111 daga cikin jirage 5,513.

Ya gargadi kamfanonin jiragen sama da cewa hukumar ba za ta lamunci ci gaba da irin haka ba.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp