Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf ya nada jarumi a masana'antar Kannywood Sani Danja mukami a gwamnatinsa
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Gwamnan Malam Sanusi Bature Dawakin Topa ya fitar, ta ce Gwamnan ya amince da nadin Sani Musa Danja a matsayin Mai ba da shawara ta musamman kan matasa da wasanni.