Sanatocin Kudu maso Kudancin Nijeriya sun bayyana goyon bayansu kudirin dokar haraji da Shugaba Tinubu ya gabatarwa majalisar kasar.
Sanatocin su ne waɗanda suka fito daga jihohin Akwa Ibom, Bayelsa, Edo, Cross River, Delta da jihar Rivers.
Cikin wani bayani da shugaban dandalin sanatocin Kudu maso Kudu Sanata Seriake Dickson ya fitar a Abuja, sanatocin sun jaddada kudurinsu na ganin cewa wannan dokar ta dace da muradin kasa, musamman jin dadi da walwalar yankin Kudu maso Kudu.
Category
Labarai