![]() |
Sakataren gwamnatin Jihar Bauchi ya yi murabus |
Gwamnan jihar Bauchi Bala Muhammad Abdulkadir, ya amince da murabus din sakataren gwamnatin jihar Barista Ibrahim Kashim.
A wata sanarwa da mai taimakawa gwamnan na musamman kan harkokin yada labarai Mukhtar M Gidado, ya fitar a ranar Juma'a, ta nuna cewa murabus din ya fara aiki nan take.
Sanarwar, ta kuma umarci shugaban ma'aikatan gidan gwamnatin jihar Dakta Aminu Hassan Gamawa, da ya rike mukamin a matsayin rikon kwarya ba tare da bata lokaci ba.