Wasu bayanai sun bayyana dangane da kasafin kudin shekara ta 2025 da ya kai naira milyan 47 da shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya gabatar.
Kamar yadda jadawalin ayyukan majalisar su ka nuna, kwamitin kasafin kudi zai gabatar da rahotonsa ne a ranar 31 ga watan Janairu 2025, abinda zai share fagen amincewa da kasafin kudin a watan Fabrairu.
Jadawalin ya nuna cewa ma'aikatu da hukumomin gwamnati za su fara kare kasafin kudinsu ne a ranar 7 ga watan Janairun 2025.