Sai nan da makonni za a fara ganin saukin man fetur - Kungiyar dillalan man fetur

 

Kungiyar dillalan man fetur na Nijeriya PETROAN ta ce 'yan Nijeriya su fara tunanin samun fetur mai sauki cikin makonni masu zuwa.

A makon jiya ne kamfanin mai na kasa NNPCL da kuma matatar mai ta Dangote su ka sanar da rage farashin man fetur zuwa naira 899.

Ganin cewa har yanzu 'yan Nijeriya ba su fara ganin farashin ya ragu ba a gidajen mai, kungiyar dillalan man ta ce hakan na faruwa ne saboda har yanzu akwai wadanda ba su sayarda tsohon mai da su ka saya da tsada ba

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp