Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta kama wasu mutane 3 da makudan kudade da suka kai naira biliyan 129 da ake zargin na bogi ne.
Kakakin rundunar, SP Abdullahi Kiyawa, ya tabbatar wa manema labarai cewa kuɗaɗen sun hada da dalar Amurka, CFA da kuma naira, kuma an sato su ne a wurin wani dake harkar kudaden kasashen waje.
SP Kiyawa ya ce mutum 2 da aka kama da kuɗin tare da wanda su ka yiwa satar duk suna tsare a hannun rundunar 'yan sanda, kuma ana ci gaba da bincike domin gano wanda ke buga kudaden na bogi.
Category
Labarai