Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta kama mutane biyu da ake zargi da satar Keke-napep


Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta kama wasu mutum biyu da ake zargi da satar Keke-napep tare da hannunta ababen hawan da ta gano ga masu su.

A cewar wani bayani da kakakin rundunar SP Abdullahi Haruna ya fitar, rundunar ta samu wannan nasara ne bayan wani samame da ta kai a maboyar bata garin da ke karamar hukumar Dambatta a ranar 9 ga watan Disamban da muke ciki.

A yayin samamen an kama wani Ado Yusuf, mai shekaru 40 da kuma Rabi’u Suleiman, mai shekaru 35, tare da kwato Keke-napep biyu da aka sace.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp