Jam’iyyar PRP a Nijeriya ta tabbatar da shirin ta na yin maja da jam’iyyar ADC gabanin babban zaben shekarar 2027.
Shugaban jam’iyyar PRP na kasa Falalu Bello ne ya bayyana hakan a wani taro na hadin gwiwa da takwararta ta ADC, da ya gudana a karshen makon nan a Abuja.
Wannan mataki dai na zuwa ne kwanaki uku bayan da jam’iyyar APC mai mulki ta yi gargadin cewa babu wata hadaka da jam'iyyun adawa za suyi da zai sa su iya kwace kujerar shugaban kasa Bola Tinubu a zaben 2027.
Category
Labarai