Ofishin Jakadancin Amurka a Nijeriya ya sanya sabbin ka'idoji ga masu neman visa


Ofishin Jakadancin Amurka a Nijeriya ya sanar da cewa ya sabunta ka'idojin da ake bi wajen karɓar izinin shiga kasar wadanda za su soma aiki daga ranar 1 ga watan Janairu 2025.

Daga yanzu duk wanda ke neman 'visa' dole ne ya ziyarci ofishin diflomasiyya da ke Lagos sau biyu. 

Ofishin ya bayyana hakan ne a shafinsa na X, kuma ya ce ya yi hakan ne a domin saukaka aikin da kuma rage jan lokaci saboda rashin gabatar da isassun takarardu.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp