NITDA ta gargadi Yan Nijeriya kan wata manhaja da ke satar bayanan asusun ajiya


Hukumar bunkasa fasahar sadarwa ta Nijeriya, ta yi gargadi game da wata sabuwar manhaja da ke kawo cikas ga na'ura 'Grandoreiro' wadda batagari suka kirkira domin tattare bayanan asusun ajiyar al'umma a fadin duniya. 

A wata sanarwa da tawagar kar ta kwana ta hukumar NITDA ta fitar, ta bayyana manhajar 'Grandoreiro' a matsayin wata babbar barazana ga na'urori, domin a cewar ta, za a iya amfani da manhajar wajen sarrafa wata na'urar ta daban tare da sace muhimman bayanai da suka hadar da bayanan banki ko bayanan sirri.

NITDA ta kuma bayyana cewa, akan iya samun sabuwar manhajar ne ta hanyar sakwannin kar ta kwana wato Email da kuma shafukan yanar gizo, wanda da zarar mutum ya sauke akan na'urarsa ko wayar salula, shikenan manhajar ta ketare ikon tsaro, komai ka iya faruwa.

NITDA ta yi gargadin cewa ita dai wannan manhajar ka iya haifar da asarar kudi da kuma satar bayanan sirri.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp