Niklas Suele dan wasan baya na kungiyar Dortmund |
Yayin da ta ke shirye-shiryen buga wasanta na gaba a gasar zakarun Turai kungiyar kwallon kafa ta Borussia Dortmund za ta kasance ba tare da dan wasanta na baya Niklas Suele ba, har tsawon watanni, sakamakon rauni da ya samu a kafarsa yayin gasar league a wasan da suka tashi 1 da 1 da Borussia Moenchengladbach.
Mai horar da kungiyar ta Dortmund Nuri Sahin, ne ya bayyana haka a ranar Talata gabanin wasansu da Barcelona a gasar cin kofin zakarun Turai.
A ranar 30 ga watan Nuwamba ne, Suele ya dawo daga jinyar raunin da ya samu a wasan da suka buga da Bayern Munich, a gasar Bundesliga.