Gwamnatin tarayya ta ce daga yanzu maganin cutar malaria zai kasance daya daga cikin jerin rigakafi na kasar.
Wannan na zuwa ne bayan da Nijeriya ta kaddamar da aikin bayarda maganin cutar zazzaɓin cizon sauro a jihohin Kebbi da Bayelsa, saboda cutar na janyowa kasar hasarar dala biliyan 1.1 a kowace shekara.
A cikin wani sako da hukumar lafiya matakin farko ta Nijeriya ta wallafa a shafinta na X, ta ce za a baiwa miliyoyin yara a fadin kasar kariya daga cutar malaria.