Nijeriya ta musanta yunkurin shigowa da sojojin Faransa ko ba ta damar hakar ma'adanai


Fadar gwamanatin Nijeriya ta musanta yunkurin mikawa kasar Faransa bangaren hako ma'adanai ko shigowa da sojojin kasar kamar yadda ake yadawa a kafafen sada zumunta.

A lokacin ziyarar da ya kai Faransa a kwanannan, Shugaba Bola Tinubu da Emmanuel Macron sun sanya hannu kan yarjejeniyar aiki tare domin karfafa samar da ma'adai tsakanin kasashen biyu.

Sai dai yarjejeniyar ta janyo cece-kuce a kafafen sada zumunta, inda wasu ke zargin Faransa za ta karbe bangaren hakar ma'adanai na Nijeriya.

A cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na X, mai magana da yawun shugaban Nijeriya, Sunday Dare ya ce Faransa za ta taimakawa Nijeriya ne kawai ta bangaren bincike da kuma hosasda dalibbai akan albarkatun ma'adanai na kasa.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp