Nijeriya za ta karbi kashi na farko na tallafin rigakafin cutar kyandar biri daga kasar Amurka wanda kawance kasashe kan samar da rigakafi a duniya Gavi ya bayar.
Wani bayani da shugaban kawancen Dr Sania Nishtar ta fitar, ta ce maganin ya isa Abuja a wannan Jumu'a bayan wata yarjejeniya da Nijeriya ta sanyawa hannu a watan Nuwamba domin karbar tallafin rigakafin har 305,000 da za a yi amfani da su wajen ya ki da cutar kyandar biri a kasar.
A ranar 24 Satumba ne kasar Amurka ta bayyana kudurinta na samarda tallafin rigakafi milyan 1 domin tallafawa yakin da ake yi da cutar mpox da ta addabi wasu kasashen.
Category
Labarai