Shugaban majalisar dattawan Nijeriya, Sanata Godswill Akpabio, ya bayyana cewa Nijeriya ta kai gargara lokacin da Shugaba Bola Tinubu ya karbi mulkin kasar.
Shugaban majalisar ya fadi hakan ne sa'ilin da yake jawabi a wajen wani taro da ya gudana a filin wasa na Ikot Ekpene Township dake jihar Akwa Ibom.
Sanata Akpabio ya yi kira ga 'yan Nijeriya musamman mutanen jihar Akwa Ibom da su ci gaba da mara wa Shugaba Tinubu baya musamman wannan lokaci da yake kokarin farfaɗo da tattalin arzikin Nijeriya.