Nijeriya ta damke mutum 10 da 'yan sandan kasa da kasa ke nema ruwa a jallo cikin mako ɗaya


Gwamnatin Nigeriya ta ce jami'an tsaronta sun kama mutum 10 dake cikin jerin mutanen da hukumar 'yan sandan kasa da kasa 'Interpol' ke nema ruwa a jallo, a cikin mako ɗaya kawai.

Ministan cikin gida Olubunmi Tunji-Ojo ne ya bayyana hakan a lokacin da Shugaba Tinubu ya kaddamar da wata cibiyar bincike ta zamani da aka samar ga hukumar shige da fice ta kasar.

Olabunmi ya ce wannan cibiyar za ta taimaka wajen gane masu mugunyar anniya da wadanda ke shiga kasar ba bisa ka'ida ba da kuma saka ido akan iyakokin kasar har inda babu jami'an tsaro.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp