Wani sabon rahoto ya nuna cewa Nijeriya na ci gaba da kasancewa a kan gaba a cikin jerin kasashen da suka rungumi amfani da kudaden badini wato cryptocurrency.
Rahoton, wanda kamfanin Consensys da ke bincike kan harkar kudaden yanar gizo da fasahar Web3 ya fitar a ranar Talata, ya ce Nijeriya da Indiya na kara bunkasa ta fannin amfani da kudaden cryptocurrency.
Kamfanin ya ce a binciken da ya yi, ya gano cewa kaso 99 na 'yan Nijeriya suna da masaniya akan kudin kiripto kuma kashi 98 suna da yarda akan kamfanonin yanar gizo da ke amfani da bayanansu.