Nijeriya da Nijar, da kuma Chadi da wasu makwabtan kasashe sun yi haɗaka wajen fatattakar 'yan kungiyar Lakurawa da suka addabi iyakokin kasar.
Wannan hadakar na da manufar kakkabe 'yan ta'addan da ke aiwatar da miyagun ayyuka a kasashen Nijeriya da kasashen dake kewaye da ita.
Da yake karin haske akan matakan da suke dauka, daraktan yada labarai na hedkwatar tsaron Nijeriya Manjo-Janar Edward Buba, ya shaidawa jaridar Punch cewa hadin gwuiwar kasashen wajen sintiri akan iyaka zai rufe duk wata mafaka da Lakurawa za su bi domin shiga kasashen.
Category
Labarai