'National Grid' ya sake lalacewa, karo na 12 kenan cikin shekarar 2024


Rumbun lantarki na Nijeriya ya sake lalacewa a yau Laraba, karo na 12 kenan a cikin shekara ta 2024.

Bincike a shafin yanar gizo na hukumar samar da lantarki ta kasa ya nuna cewa, zuwa karfe 2 na rana rumbun ba ya tattara lantarki, sai dai ya tattara megawat 3,087 zuwa karfe daya na rana.

A cikin wani bayani da kamfanin rarraba lantarki na Jos, ya ce rashin lantarki da ake fama da shi a jihohin da ke karkashin kamfanin ya faru ne sanadiyar lalacear babban rumbun lantarki na kasa.


 

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp