Ofishin hukumar NAFDAC |
Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna a Nijeriya ta kama wasu kayayyakin abinci marassa rajista da kudin su suka kai Naira biliyan 3.8 a wani rumbun ajiye-ajiye a jihar Legas.
Hukumar ta bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ta fitar ta shafin ta na X a ranar Talata.
Sanarwar ta ce jami'an hukumar sun kai samame a wani kantin sayar da kayayyaki a kasuwar Apongbon Oke Arin, biyo bayan wani rahoton sirri da ta samu.
Category
Labarai