![]() |
'Yan sandan Nijeriya |
Rundunar 'yan sandan jihar Taraba ta tabbatar da mutuwar mutane uku a wani rikici da ya barke tsakanin mabiya addinin kirista na majami'ar United Methodist da majami'ar Global Methodist a jihar.
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar, SP Usman Abdullahi, ne ya tabbatar da hakan a ranar Litinin, inda ya ce rikicin ya faru ne a karamar hukumar Karim-Lamido tsakanin mabiya majami'un biyu tun a ranar Lahadi.
A cewarsa, rundunar ta kama mutane shida da ake zargi da hannu a rikicin, yana mai cewa yanzu haka an tura jami'an ‘yan sanda da sojoji domin dakile aukuwar rikicin a nan gaba.