Ministan Abuja Wike ya kwace filayen tsohon shugaban kasa Buhari, Tajudeen Abbas, George Akume da wasu manyan mutane 759


Ministan babban birnin tarayya Abuja Nyesom Wike, ya kwace filaye tsohon shugaban kasa Muhammad Buhari, da kakakin majalisar dokoki Tajudeen Abbas da kuma Sakataren gwamnatin tarayya George Akume.

Hakama Wike ya kwace filayen wasu manyan mutane da kungiyoyi 759 a yankin Maitama II, Abuja saboda saboda kin biyan kudaden takardar mallaka.

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa har biyu da hukumar kula da babban birnin tarayya Abuja ta aikewa gidan talabijin na Channels.

Daya sanarwar ta ce, ministan ya yi barazanar kwace filayen jagoran marasa rinjaye na majalisar wakilai Kingsley Chinda da tsofaffin shugabannin majalisar dattawa Iyorchia Ayu da Ameh Ebute da mai tsawatarwa na majalisar dattawa Tahir Monguno; kazalika da wasu sanannun mutane 610, idan har ba su biyu kudaden ba cikin makonni biyu.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp