Miji da mata sun rasa ransu cikin dare a Kano

Motar hukumar kashe gobara ta jihar Kano 

Hukumar kashe gobara ta jihar Kano ta tabbatar da mutuwar miji da mata sakamakon tashin gobara cikin dare a gidansu da ke yankin Rangaza a ƙaramar hukumar Ungoggo ta Jihar. 

Babban Daraktan hukumar na jihar, Hassan Muhammad ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar Saminu Abdullahi, ya fitar ranar Juma'a a Kano. 

A cewar sa, gobarar ta tashi cikin daren Alhamis ne, inda ta kone mutumin mai suna Muhammad Uba dan shekara 67 da matarsa Fatima mai shekara 52.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp