Matsalar karancin kudi ta ta’azzara a jihohin Kano, Kaduna da Katsina

Kudi

Yayin da ya rage saura mako biyu a fara bikin Kirsimeti, mazauna jihohin Kano, Kaduna, da Katsina na fuskantar matsalar karancin kudi a hannu, lamarin da ya kara ta'azzara wahalhalun rayuwa.

Bayanai na nuni da cewa, matsalar ta jefa mazauna jihohin cikin damuwa, inda su ke rokon gwamnati da hukumomin da abin ya shafa kan su dauki mataki akan matsalar, a cewar jaridar Solacebase

A jihar Kaduna, masu sana'ar POS sun koka da cewa ba sa samun kudi fiye da naira dubu 20 a bankuna, abinda ke kara haddasa karancin kudin tun daga farkon watan Disambar nan.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp