Shugaban kamfanin mai na Nijeriya NNPCL Malam Mele Kyari ya bayyana cewa matatar mai ta birnin Warri da ke jihar Delta ta soma aiki.
Kyari ya bayyana hakan ne a lokacin da ya kai ziyarar duba a matatar tare da wata tawagar ma'aikata a Litinin din nan.
A cewarsa duk da cewa ba ta fara aiki kashi dari ba, suna kokarin aiwatar da abin da mafi yawan mutane ke ganin ba zai yiwu ba.