Matatar mai ta Dangote |
Matatar mai ta Dangote ta sanar da fara fitar da man fetur zuwa kasar Cameroon.
Wannan ci gaba da aka samu na zuwa ne bayan wata hadin gwiwa tsakanin matatar da kuma kamfanin mai na Neptune da ke Cameroon.
A cewarsu wannan hadaka za ta kara karfafa dangantakar tattalin arziki tsakanin Nijeriya da Kamaru tare da habaka samar da makamashin da yankin ke bukata.
Shugaban rukunin kamfanonin Dangote, Aliko Dangote ya bayyana cewa, a karon farko fitar da man fetur zuwa Cameroon, abu ne da ke haska goben Afrika za ta yi kyawu.
Shi kuwa Antoine Ndzengue, mamallakin kamfanin mai na Neptune, ya jaddada bayyan hadin gwiwar a matsayin abinda zai kawo sauyi ga kasar Cameroon.
Category
Labarai