Matatar man Dangote ta rage farashin litar fetur zuwa Naira 899


Matatar mai ta Dangote ta rage farashin man fetur zuwa naira 899.50 domain saukakawa 'yan Nijeriya, gabanin bukukuwan kirsimeti da sabuwar shekara.

A cikin wani bayani da mai magana da yawun kamfanin Anthony Chiejina ya fitar, ya ce kamfanin ya rage farashin ne domin rage musu yawan kudin da za su kashe wurin zirga-zirga.

Ko a watan Nuwamba matatar Dangote ta rage farashin man fetur zuwa naira 970 akan kowace lita.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp