Matar hamɓararren shugaban kasar Siriya, Bashar Al'assad ta nemi takardar saki domin ta koma Burtaniya
Asma al-Assad, matar hambararren shugaban kasar Siriya Bashar al-Assad ta shigar da karar neman saki daga mijinta tare da neman komawa kasarta Burtaniya.
Jaridar Jerusalem Post ta ruwaito cewa Asma al-Assad ba ta jin dadin rayuwar gudun hijira da take yi tare da mijinta a birnin Moscow.
Ana dai zargin cewa Asma ta shigar da kara a gaban wata kotun kasar Rasha inda ta nemi izini ficewa daga kasar, yayin da mahukuntan kasar Rasha ke duba bukatarta, a cewar kafar yaɗa labarai ta NDTV.
Category
Ketare