Matar da ta dawo da N748,320 ta samu kyautar N500,000 a Katsina

Dikko Umar Raɗɗa 

Gwamnatin jihar Katsina ta baiwa wata mata mai suna Malama Abdulkadir Yanmama kyautar kudi har naira dubu 500,000 bisa dawo da wasu kudi da aka tura mata bisa kuskure naira dubu 748,320 na shirin ciyar da makarantu na gwamnatin tarayya a jihar.

Babban daraktan hukumar kula da zuba jari na jihar Dakta Mudassir Nasir ne ya mika kyautar ga matar.

Kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya NAN ya ruwaito cewa matar dai bata cikin matan da aka zaba su dinga yin abinci ga yara yan makaranta, sai ta yanke shawarar mai da kudin ga hukumar.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp