Kungiyar mata masu zaman kansu ta Najeriya NSWA ta yi kira ga hukumomin tsaro da su kare mambobinta a fadin kasar daga tsangwama da cin zarafi da suke fuskanta, daga jami'ai da abokan huldarsu.
Kungiyar ta yi wannan roko ne a cikin wata sanarwa da kodinetar ta ta kasa, Amaka Enemo, ta fitar ranar Talata a Legas, inda ta ce wasu rahotanni na baya-bayan nan sun nuna yadda mambobinsu ke fuskantar cin zarafi daga abokan hulda da kuma jami’an tsaro.
Ta bukaci jami'an tsaro da su fahimci cewa suma yan Adam ne ba dabbobi ba, adon haka akwai bukatar suma a martaba su kamar kowa.