Masu sana'ar 'DJ' sun yi zanga-zanga ga hukumar Hisbah a Katsina

Masu sana'ar DJ da ke nishadantar da taron mutane a lokuttan bukukuwa sun cika makil a filin taro na Kangiwa Square a jihar Katsina, inda suka yi zanga-zanga ga hukumar Hisbah ta jihar bisa dakatar da sana'ar su da ta yi na tsawon watanni 8.

Masu sana'ar sun ma roki gwamnatin jihar Katsina da ta sa baki a bar su, su ci gaba da gudanar da sana'ar su da suka ce ba su takura wa kowa kuma ba su shiga hakkin kowa. Sun kuma koka kan cewa hukumar Hisbah din ta kwace musu kayan aiki na milyoyin Nairori.

Zanga-zangar ta su, ta yi daidai da lokacin da Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umaru Radda ke bude aikin fadada titin Kofar Soro zuwa Kofar Guga cikin kwaryar birnin Katsina da aka kammala kamar yadda gidan talabijin na Channels ya rawaito.

An dai ga matasan dauke kwalaye masu rubutun da ke nuna irin halin da suka ce suna ciki tun bayan dakatar musu da sana'ar da hukumar ta Hisbah ta yi.

Post a Comment

Previous Post Next Post

Kasance da DCL Hausa a kan manhajar WhatsApp